1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalolin tsaro na barazana ga zaben Najeriya

Muhammad Bello ZMA
December 9, 2022

Rahoton cibiyar Tony Blair ta kasa da kasa da ke sa ido kan salon gudanarwar gwamnatoci ya nuna cewar, demokaradiyyar Najeriya na fuskantar barazana da ka iya nakasa samun sahihin zaben 2023.

https://p.dw.com/p/4KkHR
Daya daga cikin cibiyoyin zabe
Daya daga cikin cibiyoyin zabe Hoto: Getty Images/AFP/L. Tato

Cibiyar dai ta ce matsalolin tsaro da kuma baza labaran kanzon kurege ta kafar dandalin sada zumunta ta Internet, su ne ke kan gaba wajen haifar da wannan barazanar.

Cibiyar Tony Blair mai zaman kantan dai ta karfafa cewar lallai lokaci na kure wa Najeriyar na cewar hukumomi su yi abin da ya kamata don samun nasarar zabubbukan kasar da ke karatowa na 2023. Ta nunar a rahotonta cewar, matsalolin tada kayar bayan kungiyoyin Boko Haram da 'yan rajin ballewa daga Najeriya don kafa kasar Biafra, da 'yan fashin daji da kan yi garkuwa da jamaa, da kuma 'yan bangar siyasa gami da 'yan baza labarun kanzon kurege ta kafar sada zumunta na Internet, na zaman manyan batutuwa da bai kamata hukumomin kasar su kauda ido kansu ba, domin gadan gadan cibiyar ta ce sun dau turbar haifar da kancal ga zabukan.

Rahoton dai ya jaddada matukar mahimmancin zabukan Najeriyar ga makomart da ma makomar nahiyar Africa. Dakta Kingsley Uzoma jami'i ne a kamfanin tsaro mai zaman kansa na Eagle Rescue and Alarm Systems Ltd.

Jami'an 'yan sandan Najeria
Jami'an 'yan sandan NajeriaHoto: Getty Images/AFP/U. Ekpei

Ya ce "Bayan ma barazanar kungiyoyin Boko Haram da 'yan rajin Biafra ta IPOB da 'yan Bandit, jahohin kasar tuni suke da 'yan bangar siyasa, kamar 'yan sara suka a Bauchi, 'yan bangar kuma da 'yan siyasa ke daure wa gindi. In ka je yankin Kudu maso yamma, akwai wata kungiya ta direbobin NRTW wadda karara mambobinsu 'yan tasha ne masu fushi da fushin wani da su ma 'yan siyasar ke tare da su.

Yankin Kudu maso Gabashin kasar dai , nan ne inda 'yan rajin Biafra na IPOB ke ta lasar takobin ba ma za su bari a yi zaben ba, kuma sun sha yin kashe-kashe kan hakan.

Rahoton dai ya ce Najeriyar da ma ta dade cikin barazanar tsaro, da rarrabuwar kawunan kabilun kasar kan doron addini da bangaranci, da kuma tangal-tangal din tattalin arziki, yanayin kuma da ya zama wajibi 'yan kasar su nutsu don yin abin da ya kamata yayin wannan zabe na 2023.

Tsagerun kungiyar IPOB
Tsagerun kungiyar IPOBHoto: Getty Images/AFP

Akwai dai kiran da cibiyar ta yi ga hukumomin na Najeriya na su tabbatar da cewar, kauyuka da har yanzu ba su da sukuni sakamakon rashin tsaro sun kai ga samun sukuni din kafin wannan zabe.

Yanzu dai cibiyar ta Tony Blair ta ce dole ne kasashen duniya su tallafa wa Najeriya a wannan matsananciyar gaba da ta ke kai wajen aika sako ga kasar na lallai ta tabbatar an kai ga gudanar da zabukan da duniya za ta yi na'am da sakamakon su. Tare kuma da hada gwiwa da kamfanin Internet na BIG TECH don tabbatar da an kassara masu hanzarin baza labarun kanzon kurege ta Internet daura kuma da fidda tsari na hakika don hukunta masu laifuka da suka hada da na zabe cikin hanzari.