1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya na barazanar kakkabo jiragen Amurka

Abdoulaye Mamane Amadou Suleiman Babayo
July 10, 2023

A yayin da takkadama ke kara daukar dumi tsakanin Koriya ta Arewa da makwabciyarta ta Kudu, ma'aikatar tsaron Koriyar ta Arewa ta yi barazanar kakkabo jiragen leken asirin Amurka

https://p.dw.com/p/4TeGo
Shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un
Shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong UnHoto: KCNA VIA KNS/AFP

Koriyar ta Arewa ta yi barazanar kakkabo jiragen leken asirin Amurka da ke shawagi a sararin samaniyarta. Kakakin ma'aikatar tsaron kasar ya ce Pyongyang, ba za ta lamunta da duk wani abun da ya kira tsokanar Amurka da kawayenta ba, tana mai kakkausar suka kan yunkurin Amirka na samar da wani jirgin ruwan yaki da ka iya kai hari a gabar tekun yankin.

Kazalika kakakin ma'aikatar tsaron Koriyar ta Arewa ya yi gargadin duk wani abin da ka iya biyu wa baya ga matakin Amurka kan jiragenta na lekon asiri da ke shawagi a sararin samaniyar kasar.

Da suke mayar da martani Washington da Séoul, sun lashi takobin amfani da makaman Nukuliya idan har Koiriyar ta Arewa ta dauki matakan amfani da makaman kare dangi kansu.