1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EndSARS: Zargin takurawa masu zanga-zanga

November 4, 2020

A yayin da idanuwa suke dada budewa da irin ta'adin da ya biyo bayan jerin zanga-zangar neman kawo karshen ayyukan rundunar 'yan sandan SARS, jagororin zanga-zangar da magoya bayansu na fuskantar takurawa daga gwamnati.

https://p.dw.com/p/3ksUi
Nigeria Ikeja | End Sars Proteste | Demonstranten
Zanga-zangar neman kawo karshen rundunar SARS a Najeriya ta bar baya da kuraHoto: Pius Utomi EkpeiAFP/Getty Images

Jagororin zanga-zangar da aka yi wa lakabi da #EndSARS  da ta dauki hankali a Najeriyar da ma duniya baki daya cikin watan Oktoban da ya gabata dai, sun yi zargin cewa mahukuntan kasar na matsa musu lamba su da magoya bayansu. Kama daga masu gudummawa ta abinci ya zuwa ga masu tabbatar da waya ta salula na aiki da ma ragowar makada dai, sun taka muhimmiyar rawa da nufin samun nasarar zanga-zanga Lekki ta masu neman kai karshen 'yan sandan SARS.

Karin Bayani:Sharhi kan zanga-zangar Najeriya

To sai dai kuma daga dukkan alamu ana shirin ganin daban a bangare na jiga-jigan kai karshen 'yan sandan da suka fara korafin cin zarafi a bangaren mahukuntan Tarayyar Najeriya.  Ya zuwa yanzu dai wasu na fadin an hana musu damar kai wa zuwa asusun ajiya na bankunansu, a yayin kuma da guda cikinsu ta ce jami'an shige da ficen kasar sun hana mata damar fita wajen kasar a filin jirgi.
Babban bankin kasar na CBN dai ya umarci kulle asusun da ya karbi gudummawar kudi ta neman kare ayyukan 'yan sandan. Duk da cewar dai hukumomi na kasar sun ki tabbatar da sahihanci na yunkurin da ke da ruwa da tsaki da kuma bin diddigi na tushen rikicin dai, tuni jami'ai na gwamnatin suka nuna irin bacin rai ga rawa ta kungiyoyi da ma fitattun 'yan kasar wajen ruruta wutar rikicin. 

Nigeria Lagos | Protest EndSARS
Dubban matasa sun taka rawa a zanga-zangar NajeriyaHoto: Adekunle Ajayi/NurPhoto/picture-alliance

Karin Bayani: Ana cigaba da mayar da martani kan jawabin Buhari

To sai dai kuma ko ya zuwa ina gwamnatin take shirin zuwa da nufin bi na kwakkwafin abun da ya farunc, daga dukkan alamu ana shirin ganin daban cikinNajeriyar, inda rikicin 'yan sandan ke iya rikidewa ya zuwa rikici na siyasa babba. Daya bayan daya dai gwamnonin arewacin kasar da ma sarakunan Najeriyar na dada nesanta kai ga tashin hankula  da wasu ma ke fadin na da ruwa da tsaki da kokari na kawo karshen gwamnatin da ke kan mulki yanzu.
To sai dai su kansu masu takama da son ganin karshen  'yan sandan na SARS, sunce suna da goyon baya na matakan da ba su saba da tsarin shari'a ga duk wani mai laifi a cikin sunan kai karshen 'yan sandan a fadar Auwal Musa Rafsanjani da ke zaman shugaban kungiyar Amnesty International da ke a kan gaba a jeri na zanga-zangar.

Nigeria Lagos | Protest gegen Polizeigewalt
Mata sun taka rawa a zanga-zangar NajeriyaHoto: Seun Sanni/Reuters

Karin Bayani: Kirsitocin Arewa sun shawarci matasa

Majalisar zartarwa ta kasar dai ta karbi rahoton wani kwamitin ministocin yankin Kudu maso Yamma da ya ziyarci birnin Lagos, ya kuma ganewa idonsa irin girma na asarar da zanga-zangar  ta bari. Kwamitin a karkashin minista na ayyuka da gidaje na kasar, Tunde Fashola ya nemi a kai dauki ga jihar taLagos da kuma 'yan kasuwar jihar da tashin hankalin yai wa ta'adi. Akalla kadarori na kusan zambar daya ne dai Ikkon ta ce ta yi asara, a cikin rikicin da ke zaman irinsa mafi muni tun bayan yakin basasa.