Barack Obama ya soke kai ziyara a yankin Asiya
October 4, 2013Talla
Shugban Amirka ɗin dai na ci gaba da yin gargaɗi ga yan siyasar ƙasar da su nuna datako, wajen ganin an warware matsalar da ke zaman barazana mafi girma wacce tattalin arzikin kasar ke fiskanta sakamakon tsayawar harkokin gwamnati.
Tun da farko a shirya Obama zai je a ƙasar Brunei da Indunisiya inda zai halarci taron ƙasashen yanki Asiya. Shugaban Amirkan ya ce babu wani sulhu da zai yi da yan majalisun a kan kasafin kuɗi. Ya ce : ''Babu wata tattaunwa a kan wannan batu kuma Amirkawa sun gaji da wannan ɗaukar hankali na yan siyasa, babu gishiri na ba ka manda a cikin batun.''
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar