Barack Obama ya jinjinawa shugabar gwamnatin Jamus
May 23, 2010Shugaba Barack Obama ya jinjinawa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, bayan da majalisun dokoki ƙasarta guda biyu suka sa hannu akan dokar samar da euro biliyan 750, domin ceto tattalin arzikin nahiyar turai,wanda a cikki Jamus za ta bayar da tallafin euro biliyan 148, yayin da sauran cikon tallafin zai futone daga assusun bada lamuni na AMF dakuma kwamitin ƙungiyar tarayya turai.
Shugabanin biyu dai sun tattauna ne ta waya talho tsawon mintoci 20 a jiya asabar ,akan maganar daidaita al'amuran kuɗi dakuma farfaɗo da tattalin arziki nahiyar ,gabannnin taron ƙasashe masu ci-gaban massana'antu G_20 da za a yi na gaba a cikin watan yuni a birnin toronto na ƙasar Kanada.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar