1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barack Obama ya ƙudiri aniyar yaƙi da IS

Abdourahamane HassaneSeptember 11, 2014

Shugaban na Amirka ya bayyana manufofinsa na tsarin yaƙi da Ƙungiyar masu jihadi ta IS a Siriya da Iraƙi.

https://p.dw.com/p/1DACV
Obama - Rede an die Nation
Hoto: Reuters

A cikin wani jawabin da ya yi ta gidan telbijan da rediyo na ƙasar. A karon farko Obama ya ba da umarni a faɗaɗa kai hare-hare ta jiragen sama na yaƙi a Siriya da Iraƙi tare da haɗin gwiwar gwamnati Iraƙin domin karya lagon yan ta'addar.

''Manufofinmu ƙarara suke za mu ragargaza Ƙungiyar IS a kan wani tsarin yaƙi da ta'addanci na haɗin gwiwa.

ko da shi ke Obama ya ce yazuwa yanzu sojojin Amirka ba za su shiga yaƙin Ƙasa ba kamar wanda aka yi a Afganistan da Iraƙi. Amma ya sanar da cewar ya tura ƙarin sojoji 475 domin ba da horo ga sojoin Iraƙi da kuma na Ƙurdawa