Bukatar tallafa wa kasashe matalauta
June 3, 2021Talla
Kawo yanzu dai cutar corona ta kashe mutane miliyan 3 da dubu 700, daga cikin sama da miliyan 170 da suka kamu. Hadakar cibiyar nazarin annoba ta kasa da kasa ta ce, tsakanin shekara ta 1918 zuwa 1919 annobar murar H1N1, ta yi sanadiyar rayukan mutane miliyan 50, da ke wakiltar kaso daya daga cikin ukun al'ummar duniya.
To sai dai a yayin da lamura suka fara daidaituwa a kasashe kamar Amurka da Birtaniya godiya ga allurar rigakafin na COVID, har yanzu akwai kasashe masu yawa da basu da sukunin samun alluran da suke bukata.
Richard Hatchett da ke jagorantar shirin tallafin allurar ga kasashe matalauta na MDD da ake kira COVAX, ya bada misalin Peru, a matsayin kasar da lamura suka lalace na karuwar yawan wadanda ke kamuwa da corona.