1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Hilke Fischer/Ahmed SalisuMay 4, 2015

Mahukuntan Jamhuriyar Afirka Tsakiya da kungiyoyin fararen hula da masu ruwa da tsaki sun fara wani zaman na sasanta al'ummar kasar bayan shafe tsawon lokaci ana rigingimu.

https://p.dw.com/p/1FJqE
Catherine Samba-Panza
Hoto: Reuters

Taron wanda ke gudana a wannan Litinin din ya hada kan wakilai kimanin 700 da za su zauna don duba batutuwa da dama ciki kuwa har da hade an al'ummar kasar waje guda bayan tsawon lokaci da aka dauka ana zaman 'yan marina. Kazalika a duba abubuwan da suka dangaci samar da shugabanci na gari da sake gina kasar da wanzar da doka da oda da kuma fidda sabon kundin tsarin mulki a kasar.

To sai dai yayin da dama ke kallon wannan zama a matsayin wata hanya ta maido da kasar kan tafarki madaidaici da kauda zaman doya da manja da al'ummar kasar suka shafe tsawon lokaci su na yi, wasu 'yan kasar na sukar yadda aka fidda wakilan taron yayin da wasu ke aza ayar tambaya ta sharidi da za a yi amfani da shi wajen yafewa juna irin abubuwan da suka faru. Wata mazauniya kasar ta ce "an gudanar da mulki irin na kama karya kana an yi ta kashe-kashen na gilla da yin sama da fadi da dukiyar kasa, baya ga cin mutuncin mutane da aka yi. Ana son a yafewa juna duk wadannan abubuwa, shin bisa wane sharadi ne ake son mu mance da abubuwan don mu yafewa juna?"

Zentralafrikanische Republik Übergangsparlament
Zaman taron zai yi kokarin warware manyan kalubalen da kasar ke fama da suHoto: Eric Feferberg/AFP/Getty Images

To sai dai yayin da wannan mata ke wadannan kalamai, ita kuwa Aishatou Sa'ada Moukades, mai dakin guda daga cikin limanin addinin Islama a kasar ta ce su kan suna da shukin halartar wannan taro don amfani da wannan dama da nufin ganin su kwatawa kansu 'yanci bisa irin abubuwan da aka yi musu a baya inda ta ke cewar "muna son zuwa taron don mu nemi hakkimmu. Muma ai 'yan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ne amma an ci mutuncin mu Musulmai a ko ina a cikin wannan kasa kana an nuna mana wariya."

Zentralafrikanische Republik Seleka Rebellen
Tsaro na daga cikin batutuwan da za su fi daukar hankali a taron na BanguiHoto: ISSOUF SANOGO/AFP/Getty Images

A daura da wannan kuma, masu fashin baki na siyasa a kasar da ma wadanda ke sanya idanu kan abubuwan da je su koma na ganin zaman zai taimakawa kasar wajen fiddawa kanta kitse daga wuta. David Smith na daya daga cikin mutanen da ke da wannan ra'ayi inda ya ce "za a cimma abubuwa da dama masu kyau yayin wannan zama sai dai yanzu haka gwamnatin ake da ita a kasar ta rikon kwarya ce kuma irin wannan gwamnati bisa ga yadda muka sani kan kasance ba ta da karfi da kuma lokaci sosai don haka ba lallai ta iya aiwatar da irin abubuwan da za a cimma ba."

Yanzu haka dai al'ummar kasar sun zuba idanu don ganin yadda wanann zama zai kaya da ma irin batutuwan da za a amince da su wanda za su yi nuni da irin alkiblar da kasar za ta fuskanta musamman ma da ya ke yanzu haka ta kama hanyar samun sabbin shugabanni a zabukan da za a yi cikin watan Agustan da ke tafe.