1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ban Ki Moon zai koma zauren taron kan sauyin yanayi a Bali

December 14, 2007
https://p.dw.com/p/Cbtd

A dangane da rashin cimma wani tudun dafawa a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi a birnin Bali na ƙasar Indonesia, janara sakatare na MDD Ban Ki Moon ya ba da sanarwar ba zata cewa zai koma zauren tattaunawar. To sai dai ba a san irin tasirin wannan komawar ta Ban Ki Moon zuwa tsibirin na Bali zai yi ga wannan tattaunawa ba. Har yanzu dai ministocin muhalli daga ƙasashe 190 suna ƙoƙarin cimma wata matsaya guda. Ministan muhalli na tarayyar Jamus Siegmar Gabriel ya yi nuni da cewa ana samun ci-gaba a tattaunawar. Ya ce yana da kyakkyawan fata cewa za a cimma wata yarjejeniya. Har izuwa yanzu Amirka ta ki amincewa da ƙudurorin da ƙasashe masu arzikin masana´antu suka yanke na rage fid da hayakin Carbon Dioxide mai gurɓata yanayi. Su ma ƙasashen Kanada da Rasha da Japan da kuma Australiya suna nuna dari dari. Kungiyar tarayyar Turai ta yi kira da rage yawan gurbataccen hayakin da kashi 25 zuwa 40 cikin 100 kafin shekara ta 2020.