Ban Ki-Moon yayi Allah wadai ga sabbin gine gine a yankunan Palestinu da Isra´ila ta mamaye
March 10, 2010Talla
Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin ɗuniya Ban ki-Moon yayi
Allah wadai ga matakin da ƙasar Isra´ila ta ɗauka na yin wasu
sabbin gine gine 1600 a yankunan da ta mamaye a yankin
yama ga kogin Jordan .Tun can da farko dai kafin kalamun na
Ban ki-Moon, mataimakin shugaban Amirka ne Joe Biden da
ke yin ziyara a yankin Gabas ta Tsakiya ya nuna damuwarsa
akan sabbin gine gine na Isra´ila a yankin ƙudus ta
gabas.Wani kakakin Majalisar Ɗinkin Duniyar Martins Nesirky
ya shaida cewa wannan yunƙuri na Isra´ila na taka dokokin
da aka cimmawa na ƙasa da ƙasa zai sake mayar da shirin
zaman lafiyar baya da ake ƙoƙarin cimma a yankin na Gabas
ta Tsakiya abinda kuma ya ce ba alheri ba ne ga ƙasar ta
Isra´ila .
An shirya dai nan gaba ƙadan Mista Ki-Moon zai ziyarci ƙasar
ta Isra´ila da yankin Gokin Jodan da kuma yankin Gaza.Tun
can da farko dai ƙasashen Isra´ila da Palesɗinu sun amince
da wani shirin tattaunawa na watannin huɗu a ƙarƙashin
jagorancin Majalisar Ɗinkin Duniya,a ranar litinin ne da ta
gabata ministan harakokin tsaro na Isra´ila ya bayar da izini
ga Ban Ki-Moon da wakiliyar ƙungiyar Tarayya Turai kan
harakokin waje Catherine Ashton da su kai ziyara a yankin na
Gaza. Mawallafi: Abdurrahman Hassane
Edita: Yahouza Madobi
Talla