1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ban Ki-moon ya yi gargadi ga Salva Kiir

Mouhamadou Awal BalarabeJuly 27, 2016

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya nemi Salva Kiir ya yi sara ya na duban bakin gatari kan nade-naden mukaman siyasa musamman na mataimakin shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/1JWNC
Ban Ki-moon in Südsudan
Hoto: Reuters/J. Solomon

Majalisar Dinkin Duniya ta ja hankali shugaban kasar Sudan ta Kudu kan wajibcin yin la’akari da yarjejeniyar zaman lafiya da ta bada damar kawo karshen yakin basasa a lokacin da yake nade-naden mukamai. Wannan gargadi ya zo ne bayan da Shugaba Salva Kiir ya nada Janar Taban Deng Gai a matsayin sabon mataimakin shugaban kasa.

Dama dai yarjejeniyar zaman lafiya ta ware wannan mukami ga bangaren 'yan tawaye da ke adawa. Sai dai kuma akwai baraka tsakanin Taba Deng Gai da wanda ya gada wato tsohon mataimakin shugaban kasa. Shi dai Riek Machar.da ke zama madugun 'yan tawaye ya bar kasar Sudan ta Kudu a farkon wannan watan, bayan da tashin hankali ya barke tsakanin magoya bayansa da kuma na shugaban kasa Salva Kiir.