Gwajin nukiliya tsokana ce da gangan
September 9, 2016Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya bukaci kwamitin sulhun majalisar ya dauki matakin da ya dace domin maida martani a kan gwajin makamin nukiliya karo na biyar da Koriya ta arewa ta yi.
" Ya ce Ina Allah wadarai da kakkausar lafazi gwaji na karkashin kasa da na makamin nukiliya da Jamhuriyar Koriya ta arewa ta yi, wannan wani keta kudiri ne na kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da gangan".
Ban Ki-Moon ya ce wajibi ne a dauki matakin dakile irin wannan takala cikin gaggawa.
Kafar yada labaran gwamnatin Koriya ta arewan dai ta ce gwajin wanda aka yi shi bayan gwajin wasu jerin makamai masu linzami, sun cimma burin kasar na iya dasa dangon makamin nukiliya a kan makamin roka.
Kwamitin sulhun dai ya sha alwashin daukar matakin ladabtarwa a kan Pyongyang.
Japan ta bukaci a sanya wa Koriya ta arewar sabbin takunkumi sai dai kuma China wadda babbar aminiya ce ga Pyongyang ta ce ya kamata a yi taka tsantsan domin kauce wa rura wutar rikici a yankin na tsibirin Koriya.