Ban ki Moon ya baiyana takaicinsa game da rashin cimma matsaya a taron Bali
December 15, 2007Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya fadawa mahalarta taron Majalisar Dinkin Duniya kan canjin yanayi dake gudana a Bali cewa sun bada shi,tun da ba a samu cimma yarjejeniya ba kawo yanzu. Ya roke su da su yi anfani da wannan dama domin taimakon alumma.Sakataren na Majalisar dinkin duniya ya kai ziyara ce ta ba zata wajen taron a yau asabar yayinda aka kara kwana guda kann waadin taron a kokarinsu na cimma matsaya guda kan matsalar canjin yanayi. Ya zuwa yanzu dai kasashen turai da Amurka sun daidaita kann yawan hayaki mai guba da zasu rika fitarwa. Kungiyar Tariyar Turai dai tana neman kasashe masu arzikin masanaantu da su yi kokarin rage hayakin masanaantun nasu da kashi 40 cikin 100 nan zuwa shekara 2020 batu kuma da Amurka ta ke adawa da shi. Na dai shirya taron na Bali ne da nufin kaddamar da shawarwari kann wata sabuwar yarjejeniya shekaru biyu kafin karewar waadin yarjejenjar Kyoto a 2012.
AFGHANISTAN