1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ban Ki Moon na fuskantar adawa

Zainab A MohammadFebruary 8, 2007

Kungiyoyi masu zaman kansu sunyi adawa

https://p.dw.com/p/BtwK
Sakatare General Ban Ki Moon
Sakatare General Ban Ki MoonHoto: AP

Sakatare general na majalisar dunkin duniya Ban Ki Moon,wanda a watan daya gabata ya tabbatar da muhimmancin kungiyoyi masu zaman kansu wajen samarda zaman lafiya a nahiyar Afrika,na fuskantar matsaloli daga kungiyar hadin gwiwar kungiyo masu zaman kansu,a shirinsa na sake yiwa sashin kula da harkokin kwance makamai na majalisar garon bawul.

Hadin gwiwar kungiyoyi masu zaman kansu guda 12 sun bukaci kasashe dake da wakilci a mdd dasu nuna adawarsu da wannan yunkuri,suna masu cewa rusa wannan sashi zai kawo mata cikas cikin kokarin sauke nauyi daya rataya a wuyanta,musamman ma na ganin cewa an kwance damarar yaki a sassa daban daban da ake fama da rigingimu.

Tawagar wadda ta aike da wasika ga kasashe 192dake da wakilci a majalisar , ta hadar da kungiyar komitin lauyoyi dake lura da harkokin makaman nucklear,da kungioyar mata ta kasa da kasa dake fafutukar ganin an samarda zaman lafiya,da kungiyar kare yake yake da ta tsara hadin kkannduniya ,da kuma hadaddiyar kungiyar na dake yaki da yaduwar kananan makamai a dorin kasa,da kuma kuma komitin dake kula da harkokin tsaro da zaman lafiya.

Akasarin wadannan kungiyoyi dake wakiltar kungiyoyi masu zaman kansu dake da cibiyoyi a birnin New york din Amurka,na aiki ne kann batutuwa dasu hadar da kwance makamai da tsaro a tsarin mdd.

A ranar litin daya gabata nedai Mr Ban ki Moon ya gabatarwa zauren majalisar wannan kuduri nasa na sauya wannan sashi ,zuwa ofishin kula da hartkokin kwance damarar yaki,wadda zatayi aik8i kai tsaye dashi.

Ya kuma sanar dacewa wakilin shi na musamman ne zai zai shugabanci wannan ofishi.Sai dai bai ambaci matsayin maishi ba,batu da ake gzargin cewa ya rage matsayin wannan sashi.A yanzu haka dai mataikin sakatare general na mdd na biyu ne ke shugabantar wannan sashi,mutumin dake zama na uku a tsarin majalisar.

Da aka nemin jin ta bakinsa adangane da yiwuwar hannun Amurka kokarin rage matsayin wannan sashi,babban directa na komitin lauyoyi dake kula da shirin nuclear mai cibiya a New York John Burroughs,ya bayyana cewa bashi da wata masani a dangane da haka.Sai dai yace wannan yunkurti na Ban Ki Moon nada nasaba da kamfaign da wasu yan majalisar dottijai dana dokoki masu tsattsauran raayi a shekarun 1990s,na ganin cewa an soke wannan sashi dake kula da harkokin kwance makamai a mdd.

A makon daya gabata nedai kungiyar yan baruwammu mai wakilan kasashe 117,suka ki cewa komai adangane da wannan yunkuri na sakatare general na ragewa sashin kwance damarar yakin matsayi,kazalika kasashen yammaci da suka hadar da Irelan,da Sweden da Norway da Austria da New Zealand.

Wasikar da kungiyoyin suka rubuta bugu da kari tayi nuni dacewa,idan har wannan sashi yanada alaka kai tsaye da sakatare general na mdd,to babu shakka zata fuskanci matsaloli wajen gudanar da aikinta,saboda irin matsin lamba dazai samu daga bangarori daban daban,wanda zai iya kawo cikas cikin aiwatar da wasu muhimman batutuwa saboda siyasar majalisar.