1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ban Ki Moon a yankin Falasɗinawa

March 20, 2010

Masu shawarta batun Gabas Ta Tsakiya sun goyi bayan kafa ƙasar Falasɗinu

https://p.dw.com/p/MYEu
Ban Ki MoonHoto: AP

Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon wanda a yau ya fara wani rangadin yankunan Falasɗinawa da Isra´ila ya ce ɓangarorin nan huɗu dake shawarta batun Gabas Ta Tsakiya na goyon bayan ƙoƙarin Falasɗinawa na kafa ƙasar kansu. Ban ya fara wannan ziyara ta yini biyu tare da ganawa da Firaministan Falasɗinawa Salam Fayyad a birnin Ramallah na Gaɓar yammacin Kogin Jordan inda ya ganewa idonsa irin mummunan tasirin da manufar Isra´ila ta gina matsugunan Yahudawa ke yi a wannan yanki. A gun wani taron manema labaru Ban cewa yayi.

Ya ce: "Dole tattaunawar da ake yi ta kai ga kawo ƙarshen mamayen da ake yi tun a shekarar 1967. Dole a warware dukkan batutuwan dake kwance kamar matsayin birnin Ƙudus, makomar ´yan gudun hijira da na kan iyakoki. Wannan ita ce mafita kuma babu wani zaɓi. Dole dukkan waɗanda abin ya shafa su nuna halin ya kamata don samun nasarar tattaunawar."

Ana sa rai babban sakataren na Majalisar Ɗinkin Duniyar zai gana da manyan jami´an Isra´ila sannan zai kai ziyara Zirin Gaza dake ƙarƙashin ikon Hamas.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi