Ban Ki Moon a Syria
April 24, 2007Sakatare jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia, ya fara ziyara aiki ta kwanaki 2 a ƙasar Siyria.
Ban Ki Moon, zai gana da hukumomin Damascus, a game da kotun ƙasa da ƙasa da za agirka, wadda za ta shari´ar kissan tsofan Praminsitan Libanon Rafik Hariri, da kuma batun sa ido, a iyakokokin Libanaon da Syria.
Wannan ita ce ziyara farko da Ban Ki Moon ya kai a Siyria, tun bayan hawan sa, kan karagar mulki, ranar 1 ga watan janairu na wannan shekara.
Cemma ya kai irin wannan ziyara a ƙasar Libanan, inda ya bayyana wajibcin girka wannan kotu wada ƙasar Siyria ke nuna adawa da ita.
A dangane da batun sa ido ga iyakokin Syria da Libanaon Ban Ki Moon zai gabatarwa wa shugaba Bashard Al Assad na Syria buƙatar Majalisar Ɗinkin Dunia ta dakatar da shigar da makamai zuwa Libanon.
Sannan magabatan 2 za su anfani da wannan dama, domin masanyar ra´ayoyi a game da rikicin gabas ta tsakiya.