1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ban Ki Moon a gabacin Kongo da kuma Rwanda

May 23, 2013

A lokacin ziyarasa a yankin Ban ya yi nuni da cewa nauyin tabbatar da zaman lafiya da hadin kan Kongo na kan rundunar sojin kasar.

https://p.dw.com/p/18d8B
U.N. Secretary-General Ban Ki-moon is escorted by U.N. peacekeepers during his trip in Goma, in the Democratic Republic of Congo's war-torn east, May 23, 2013. Rebels in eastern Congo announced a ceasefire on Thursday in fighting with government troops hours before a visit to the conflict-plagued zone by Ban and World Bank President Jim Yong Kim. REUTERS/Jonny Hogg (DEMOCRATIC REPUBLIC OF CONGO - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Hoto: Reuters

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya jaddada a wannan Alhamis cewa dole tsaro ya tafi kafada da kafada da ci-gaba a birnin Goma mai fama da rikice rikice dake gabacin Kongo. Ban ya furta haka ne lokacin da ya isa birnin sa'o'i kalilan bayan wata kungiyar 'yan tawaye ta dakatar da fada domin ba shi damar kai wannan ziyara. Shugaban na Majalisar Dinkin Duniya ya je Goma ne a karon farko tun bayan da Kwamitin Sulhu ya ba da izinin kafa wata runduna da za a girke a birnin wadda kuma aka ba ta ikon fuskantar 'yan tawayen kungiyar M23 dake a arewcin birnin. Ban ya ce nauyin tabbatar da zaman lafiyar yankin yana kan sojojin Kongo.

"Alhakin tabbatar da zaman lafiya da hadin kan kasar jamhuriyar demokradiyyar Kongo ya rataya ne a wuyan dakarun sojin Kongo da kuma shugabanninta."

Sa'o'i kalilan gabanin isar Ban birnin na Goma, 'yan tawaye sun sanar da cewa za su girmama wani shirin tsagaita wuta don ka da su kawo cikas ga rangadin na diplomasiya. Bayan yada zango na sa'o'i biyu yanzu haka Mr. Ban ya karasa zuwa Rwanda dake makwabtaka.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Saleh Umar Saleh