1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ban Ki Moon a Chadi

September 7, 2007
https://p.dw.com/p/BuC9

Acigaba da rangadin aikinsa akasar Tchadi,Sakatare General na mdd Ban Ki Moon ya gana da shugaba Idriss Deby Itno,inda suka tattauna rikicin lardin Darfur da matslolin tashe tashen hankulan kasar Sudan, kazalika da makomar yan gudun hijira da suka tsere takan iyakokin kasashen biyu.Da safiyar yau nedai jagoran na mdd ya isa birnin Njasmena daga Khartum,bayan kammala rangadin kwanki uku a Sudan,inda ministan harkokin waje Ahmad Allanm-Mi ya marabceshi,kafin yayi ganawar saoi biyu da shugaba Deby,wanda kasarsa ke zama matsaugunin yan gudun hijiran sudan kimanin dubu 236.Shugabannin biyu sun shaidawa manema labar cewa sun cin nasarar tattauna muhimman batutuwa da suka hadar da batun tura ayarin hadin gwiwa tsakanin turai da mdd ,domin kare rayukan fararen hula dake chadi da janhuriyar afrika ta tsakiya,wadda ke hada kann iyaka ta arewaci da Tchadi kana ta darfur ,ta yammacin Sudan.