Ban Ki Moon a Afrika
September 5, 2007A cigaba da ziyara aikin sa a nahiyar Afrika, Sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Dunia Ban Ki Moon, ya bayyana damuwa, a game da sake borowar tashe-tashen hankulla a Jamhuriya Demokrdaiyar Kongo.
A wata sanarawar da ya hiddo a dangane da wannan rikici, Ban Ki Moon ya gayyaci ɓangarori masu gaba da juna su tsagaita wuta,mussamman a yankin arewanci Kivu, inda a ke ci gaba da ɓarin wuta.
A halin yanzu, da dama daga mazauna wannan yanki sun ƙaurace masa.
Ban Ki Moon, ya bada ƙarfin gwiwa ga taron ministocin harakokin wajen Ruanda da na Jamhuriya Demokradiyar Kongo, wanda su ka tantana a birnin Kinshasa, a game da hanyoyin maido da zaman lahia.
ƙasashen 2, sun cimma daidaito, a game da matakin gama ƙarfi, domin kwance ɗamara yan tawayen Hutus na ƙasar Ruanda, wanda ke da alhakin tashin-tashinan da ke wakana a gabacin Jamhuriya Demokradiyar Kongo.