1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bama: Nemawa 'yan kabilar Rohingya 'yanci

Salissou Boukari
August 24, 2017

Wani kwamitin kasa da kasa da tsohon sakataren Majalisar dinkin Duniya Kofi Annan ke jagoranta ya yi kira ga hukumomin kasar Bama da su bai wa Musulmai 'yan kabilar Rohingya cikaken 'yanci a kasar.

https://p.dw.com/p/2ilgo
Rohingya in Myanmar Kofi Annan
Tsohon Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan a birnin MyanmarHoto: DW/V. Hölzl

Rahoton dai ya ce muddin ba haka ba 'yan kabilar na Rohingyas za su iya zama masu tsatsauran ra'ayi. A shekara ta 2016 ne dai bisa tambayar ministar harkokin wajen kasar ta Bama Aung San Suu Ky ne dai aka kafa wannan kwamiti wanda ya gabatar da sakamakon aikinsa a gaban hukumomin na birnin Rangoun a wannan rana ta Alhamis.

Da ya ke magana kan wannan batu shugaban Kwamitin Mista Annan ya ce muddin dai ba'a kai ga samun walwale bakin zaran wannan matsala cikin gaggawa ba, to akwai hadarin samun tsatsauran ra a ayi a tsakanin 'yan kabilar Rohingyas Musulmi da 'yan kabilar Bouda da ke kasar. Tuni dai kungiyoyin kare hakin bil-Adama suka yaba da sakamakon wannan rahoto. A 'yan shekarun baya-bayan nan dai tsirarun Musulman kasar ta Bama 'yan kabilar Rohingyas na fuskantar cin zarafi mai tarin yawa a kasar.