Bakin haure sun rasa rayukansu a Yemen
June 14, 2021Talla
Kifewar kwale-kwalen na kasancewa mafi munin hatsari na baya-bayan nan da ya rutsa da bakin hauren da suka fito daga nahiyar Afirka don neman rayuwa mai inganci a kasashen yankin Gulf masu arzikin man fetur.
Rahotanni na nuna cewa kwale-kwalen ya taso ne daga kasar Jibuti dake gabashin Afirka inda ya nutse a yankin Ras al-Ara da ke lardin Lahj na kasar Yemen. Sai dai har kawo yanzu babu rahoton da ya ce wasu sun rasa rayukansu ko ma an ceto wasu. Ko a watan Afrilun da ya gabata wani kwale-kwale dauke da bakin haure 40 ya kife a gabar ruwan Jibuti.
Dubban mutane ne dai ke gujewa talaunci a kasashen Habasha da Jibuti da Somaliya zuwa Yemen don tsallaka wa zuwa kasashen yankin Gulf.