1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bakin-haure da dama sun mutu a tekun Bahar Rum

Suleiman BabayoAugust 5, 2015

Ma'aikatan agaji na ci gaba da neman wadanda suka tsira sanadiyar hadarin jirgin ruwa mai dauke da bakin-hauren da suka fito daga Libiya.

https://p.dw.com/p/1GAko
ESA - Erste Bilder des Sentinel 2 Satelliten
Hoto: Copernicus data/ESA

Jami'ai da kungiyon agaji sun bayyana cewa an tsamo gawawwaki 25, yayin da aka samu wasu mutane kimanin 250 da rai, kamar yadda hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta nunar, daga cikin kimanin bakin-haure 700 da jirgin ruwansu ya kife a tekun Bahar Rum bayan fitowa daga kasar Libiya.

Ana fargabar mutane masu yawa sun gamu da ajalinsu sakamakon hadarin. Jiragen ruwan kasashen Turai masu aikin ceto na cigaba da neman wadanda suka tsira.

Cikin shekarar da ta gabata ta 2014 kimanin mutane 3,300 suka mutu a yunkurin tsallakawa Turai ta tekun Bahar Rum, yayin da a wannan shekara zuwa wannan lokaci fiye da 2000 suka bakunci lahira. Galibi bakin sun fito daga kasashen Afirka da kuma yankin Gabas ta Tsakiya, inda suke guje wa yake-yake da talauci.