1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babu tabbas na asalin maharan wuraren ibada

March 1, 2012

Cece kuce dangane da kama wasu matasan kiristoci su bakwai da aka kama bisa zargin yunƙurin kai harin bam akan wani coci a jihar Bauchi dake arewacin Najeriya.

https://p.dw.com/p/14Cp9
Hoto: Picture-Alliance/dpa

Har yanzu ana ta kai ruwa rana, dangane da kama wasu matasan kiristoci su bakwai da rundunar 'yan sanda ke tsare da su saboda wani yunkuri da aka ce sun yi na dasa wani bam a wata majami'a a garin Miya Barkatai a cikin ƙaramar hukumar Toro a jihar Bauchi dake arewacin Nigeria.

Ƙungiyar kiristoci reshen jihar Bauchi sun gudanar da wani taron manema labarai, inda suka ce da sake, a rahoton 'yan sanda na kama waɗannan matasa da ake zargin suna ɗauke da bam, a cewar shugaban ƙungiyar reshen jihar Bauchi, Rev. Lawi Pokti.

Ya ce akwai abin dubawa a wannan magana ko zargi. Rev. Lawi yayi ƙarin bayani akan abin da suka fahimta yana mai cewa.

"Abin da ya faru a Miya Barkatai shi ne a bayan rikicin zaɓen shugaban ƙasa  da aka yi, an ƙona wata majami'a, kuma ana ta taruka akai akai ta yadda za'a yi wannan gini, shi ne matasa suka tashi domin su yi tambaya ana zama ana zama, ina ne matsayin zaman da ake yi?"

Rashin imani ne kai hari bam akan wuraren ibada

Ya ƙara da cewa shi bai ga bam da ido sa ba, "amma hukuma ta ce akwai bam, idan kuma akwai wanda ya zo da bam to wannan rikicin zuciya shedanci ne, kafirci ne, rashin jin maganar Allah ne, domin muma inda gaske ne ya zo da bam, to ina ganin baya da ruhun Allah a jikinsa, bai san Yesu ba, bai san Allah ba, inma yana zuwa masajida, to ni yana zuwa masajida ne kawai amma shi ba mai tsoron Allah bane."

Generalvikar Peter Ebidero steht am 10.03.2007 vor der katholischen Kirche in Kano im mehrheitlich muslimischen Norden Nigerias. Anders als im Süden gilt hier die islamische Rechtssprechung, die Scharia. Christen haben es hier sehr schwer, die Universität zu besuchen oder eine Arbeit zu finden. Foto: Ulrike Koltermann (zu dpa-Reportage: "Halleluja-Hysterie und Scharia in der religiösesten Nation der Welt" vom 21.03.2007) +++(c) dpa - Report+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Su kuwa ana su fannin ɗaya daga cikin malaman ƙungiyar Islama masu da'awa da kula da waɗanda suka musulunta, Mallam Ibrahim

Hassan Jahun, cewa yayi, a yadda abubuwa ke aukuwa a halin yanzu a Nijeriya, kamata yayi mahukunta su yi aikinsu in ana son zaman

lafiya a ƙasa da kuma nemo bakin zaren hare haren bam da ake kaiwa a wasu sassan ƙasa. Ya ci gaba da cewa:

"Domin duk wani abin da aka ce an yi a coci, ko za a yi, domin saɓanin da suka ce a tsakaninsu, wannan bai kai ga za a ɗauki matakin kai bam zuwa ga coci ba, domin duk inda bam ya tashi a irin wannan ƙasa, akan huce ne akan cewa musulmi suka yi, har a ɗau mataki kamar abin da ya faru a cocin nan na Jos, wanda aka kai hari ga musulmi dake garin Jos. Wannan hari a nan Miya Barkatai, da ya faru, da babu shakka abin da za a ɗora akai shine musulmi ne."

Aiki na gaskiya shi ne mafita daga rigingimu a Najeriya

Ni a nan abin da nike jan hankalin mahukunta a wannan ƙasa ta mu shi ne su tsaya fa a yi aiki na gaskiya, domin magance waɗannan matsaloli, in ba haka ba, ba za a taɓa magance matsalar ba. Kamar yadda ya faru a Yenagoa, wanda aka samu wani mutum yayi shigar musulunci an kama shi da makami yaje zai sa bam a coci, wannan ya nuna da yayi nasara, da za a ce musulmi suka yi, sa'annan abin da ya faru a jihar Gombe, wanda aka kama mutum biyu da makamai, su ma da sun kai ga nasarar abin da suka yi za a ce musulmi ne. Don haka jami'an tsaro su tsaya su yi aikin da za a magance rayukan ɗinbim talakawa da ake kashewa akan wannan al'amari wanda yake babu wani mutum wanda yake da addini wanda ya san abin da yake yi da zai goyi bayan wannan abu.''

Vor den Polizeiposten in Nordnigeria bilden sich oft kilometerlange Autoschlangen. Copyright: Katrin Gänsler Kano, Nigeria, 06.02.2012
Hoto: Katrin Gänsler

Tuni dai an umarci rundunar 'yan sandan jihar Bauchi da su kai matasan da ake tsare da su ake zargin, zuwa Abuja domin ci gaba da bincike a samu gaskiyar maganar.

Mawallafi: Ado Abdullahi Hazzad
Edita: Mohammad Nasiru Awal