1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babu alamun lafawar rikicin Turkiyya da PKK

Mohammad Nasiru AwalNovember 16, 2015

Sojojin Turkiyya sun kashe 'yan tawayen Kurdawa 13 a wani farmaki da jiragen saman yakinsu suka kai a kudu maso gabacin kasar.

https://p.dw.com/p/1H6qs
Türkei Kurdistan Diyarbakir PKK Kämpfer
Hoto: Getty Images/AFP/I. Akengin

Dakarun tsaron kasar Turkiyya sun kashe 'yan tawayen Kurdawa 13 a wani hari ta sama da suka kai a yankin kudu maso gabacin kasar da ke kan iyakarta da Iraki. Hakan na zuwa ne daidai lokacin tashe-tashen hankula ba su nuna alamun lafawa tsakanin bangarorin guda biyu ba. Rigingimu sun ta'azzara musamman a yankin Kurdawa tun a watan Yuli lokacin da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma da kungiyar PKK ta rushe, abin da ya yi sanadiyyar rayukan daruruwan mutane kuma ya gurgunta shirin zaman lafiya da gwamnatin birnin Ankara ta ayyana da jagoran kungiyar a karshen shekarar 2012. Tuni dai shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya lashi takobin yakar kungiyar ta PKK har sai ya tarwatsa "dukkan 'ya'yanta masu ta da kayar baya".