Babu alamun kawo ƙarshen matsaloli a PDP
January 12, 2011Aski dai ya zo gaban goshi a jam'iyar ta PDP da ke jan ragamar mulki a tarayyar Najeriya game da fid da gwanin da zai tsaya mata takara a zaɓen shugaban kasa da zai gudana a watan Afrilu mai zuwa. A daidai lokacin da ya rage sa'o'i ƙasa da 24 a gudanar da taron da zai bayar da wannan dama, manyan ɓangarorin jam'iyar ta PDP na fafatawa da juna da nufin zama gwani a taron da zai gudana a birnin Abuja. Ana wata sai kuma ga wata a ranar Laraba wata kotu da ke garin Inugu na kudacin Najeriya ta yanke hukuncin dakatar da shugaban jam'iyar PDP Chief Nkosilezi Nwodu daga muƙaminsa.
A ƙasa za ku iya jin ƙarin bayani a cikin rahotannin da wakilanmu a Abuja Ubale Musa da kuma Uwais Abubakar Idris suka aiko mana.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Ahmad Tijani Lawal