COP25: An gaza cimma matsaya a taron sauyin yanayi
December 14, 2019Talla
Taron wanda ya kamata a kammala ranar Juma'a an tsawaitashi har ya zuwa ranar Asabar (14.12.19) saboda rashin jituwar da aka samu tsakanin kasashen wajen rage hayaki mai illa ga muhali da maki biyu kamar yadda yarjejeniyar da aka cimma a Paris a shekara ta 2015 ta tanada.
Kasashen China da Indiya da Japan da Amirka da ke kan gaba wajen fitar da hayakin mai guba ba su kai ga amincewa da dokokin da taron ya tattauna a tsawon makonnin biyun a aka share ana gudanr da shi a birnin Madrid na kasar Spain ba.