1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guterres ya bude babban taron MDD na bana

September 21, 2021

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya bude babban taron majalisar na bana a birnin New York a wannan Talata. Wannan shi ne karo na farko da ake yin taron gaba-gaba da a cikin kusan shekaru biyu.

https://p.dw.com/p/40cyG
United Nations Generalsekretär Antonio Guterres
Hoto: John Minchillo/AP/picture alliance

 

A yayin bude taron Guterres ya nuna damuwa kan rashin daidaiton da ake samu wurin mallakar rigakafin cutar corona a tsakanin kasashen duniya, yana mai siffanta lamarin da cewa ba abu ne da za a amince da shi ba. Guterres ya nuna bacin ransa kan yadda manyan kasashen duniya suka kusan kammalawa yi wa mutanensu rigakafi a yayin da kaso 90 cikin 100 na kasashen Afirka ba suka kai ga mallakar rigakafin ba.

''Duniyar mu ta shiga wani hali, kama daga matsalar sauyin yanayi da fitintinu da kuma cutar corona, gwiwowinmu za su iya yin sanyi amma ba mu saduda ba. Zabi yana gare mu, za mu iya gyarawa ta hanyar samar da fata nagari a tsakaninmu.'' inji Guterres

Shi ma da yake na sa jawabin Shugaban Amurka Joe Biden ya bukaci kasashen duniya su hada hannu don yaki da corona da sauyin yanayi da kuma rigingimun da ke gudana a Habasha da sauran wurare.