1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban sakataran MDD ya yi jawabi akan Siriya

January 15, 2012

Ban Ki Moon ya gargaɗi shugaba Bashar Al Assad da ya dakatar da kashe al'ummar sa

https://p.dw.com/p/13jzP
NEW YORK, Aug. 27, 2011 UN Secretary-General Ban Ki-moon speaks to media during a press conference at the headquarters in New York, the United States, Aug.26, 2011. After a meeting with heads of regional organizations on Friday afternoon, Ban told reporters that the international community, including the UN, stands prepared to provide support to Libya in the aftermath of its violent, months-long conflict
Ban Ki-Moon babban sakataran Majalisar Ɗinkin DuniyaHoto: picture alliance ZUMA Press

Babban sakataran MDD Ban Ki Moon ya buƙaci shgaban ƙasar Siriya da ya kawo ƙarshen kisan gilar da ya ke aikata wa kan al'ummar sa ''ya ce a yau na ƙara jadada cewar da shugaba Bashar Al Assad da ya dakatar da kisan jama´ar sa,

Ya ce kuma tarihi ya nuna cewar babu wani shugaba da ya riƙa amfani da ƙarfin dawo dawo akan al´ummar sa kana kuma ya sha salin alin.Mista Ban Ki Moon wanda ya baiyana haka a wajan wani taro a birnin Berouthe na ƙasar Libanon wanda ke tattauna sauye sauyen da kuma yadda za a riƙa tafiyar da gwamntin wucin gadi ta dimokariyya wanda tsafin shugabannin ƙasashen duniya da kuma masu ci yanzu suke hallarta ya ce lokaci yayi da za a samu sauyi a Siriya.Wannan furci da babban sakataran majalisar ya yi ,ya zo ne a daidai lokaci da shugaba Assad ya baiyana wani ƙudirin doka ;da yayi ahuwa ga waɗanda ke da hannu a cikin yamutsin da aka soma a ƙasar tun cikin watan maris da ya gabata.

Mawallafi :Abdourahamane Hassane
Edita : Ahmad Tijani Lawal