1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aung San Suu Kyi ta gana da jami'in gwamnatin Sojin Burma

October 25, 2007
https://p.dw.com/p/C15g

Mai fafutukar neman kafuwar democradiyya ta kasar Burma,Aung San Suu kyi ta bar gidanta,inda take daurin talala,domin ganawa da wani babban jamiin hulda da jammaa da gwamnatin mulkin sojin kasar ta nada.An dai nada General Aung Kyi mai ritaya ne,bayan ziyarar jakadan mdd na musamman Ibrahim Gambari ,wanda ya bada shawarar hada danganta tsakanin gwamnatin sojin da mai fafutukar democradiyyar.A ranar 2 ga watan oktober nedai Ibrahin Gambari ya gana da Aung San suu Ki ,kana anasaran komawarsa kasar ta Myanmar a makon farko na Nuwamba mai kamawa.Babu bayanai dangane da sakamakon gawartata da babban jamiin gwamnatin sojin kasar,wanda ya gudana a wani gidan saukar baki na gwamnati.