1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Atiku yace a,a da tazarcen Obasanjo

Zainab A MohammadApril 6, 2006
https://p.dw.com/p/Bu74

Mataimakin shugaban kasa Atiku abubakar ,a karo na farko a bainar jammaa ,ya soki shirin tazarce a karo na ukun shugaba Olusegun Obasanjo,adaidai lokacin da adawa da shirin ke dada samun kaimi a kasar.Atiku Abubakar yayi jawabinsa da adawa da shirin tazarce din ne wa gwamnonin kasar guda biyar,taron daya gudana daga tsakar daren jiya zuwa safiyar yau,taron kuma daya samu halartan yan majalisar dokoki sama da 100 da manyan shugabanin adawa na tarayyar Nigerian.Wannan taro dai ya gudana ne a a gidan daya daga cikin gwamnonin,sakamakon yansanda sun hana a gudanar dashi a otel.Wannan ganar adawa dai tazone,saoi kalilan bayan jagoran shirin tazarcen kuma mataimakin shugaban majalisar dattijai,Ibrahim Nasiru Mantu ya tsalleke rijiya ta baya dakyar,daga yunkurin tsige shi,da yan majalisar sukayi.Mahalartan taron dai sun shaidar dacewa,Atiku Abubakar wanda ke neman kujeran Obasanjo a zaben shekara mai zuwa,ya fadawa taron cewa,da hadin kann dukkan masu adawa da shirin ,zaa iya dakatar da gabatar dashi a gaban majalisar kasar,balle ayi kuria kansa.Dangantaka tsakanin Atiku da babban uban gidansa Obasanjo dai tayi tsami ne abayyane daga watan Augustan daya gabata,amma wannan shine karo na fariko da Atikun ya kalubalanci Obasanjo a bayyane.