PDP ta yi zargin sakaci a yaki da Boko Haram
November 23, 2018A Najeriya babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta bukaci gwamnatin kasar da ta fito ta yi wa 'yan kasa bayani dalillan da suka sanya sannu a hankali hare-haren Kungiyar Boko Haram ke kara kamari a yankin Arewa maso gabashin kasar duk da matakan sojan da gwamnatin ke ikrarin dauka.
A cikin wani sakon ta'aziyya da ya aika wa iyalan mutanen da suka mutu a hare-haren baya bayan nan da Kungiyar ta Boko Haram ta kai inda ta kashe sojojin Najeriya akalla 44, Atiku Abubakar dan takarar jam'iyyar adawar ta PDP a zaben 2019 ya bayyana cewa karfin da Boko haram ke kara dauka a baya bayan nan na nuni da cewa gwamnatin ba ta samar wa da rundunar sojin Najeriyar wadatattun kudaden sayan makaman tunkarar matsalar ta Boko Haram ba.
Shi ma dai daga nashi bangare tsohon gwamnan kana kusa a jam'iyyar ta PDP Peter Ayolele Fayose ya ce lokaci ya yi da ya kamata gwamnatin Najeriya ta fito ta amince cewa har yanzu ba ta ci Boko haram da yaki ba.