Atiku ya bar jam'iyyar APC
November 24, 2017An dai dauki lokaci ana jiran tsamani kafin kai wa ga sabon matsayin da ya kai Atiku Abubakar raba auren da ke tsakaninsa da jam'iyyar APC mai mulki. A wata sanarwar da Atikun ya fitar a wannan Jumma'a, ya zargi shugaban kasar Muhammadu Buhari dama jam'iyyar APC da kama karya da rashin mutunta demokradiya. Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma ce bai shiga wata sabuwar jam'iyya ba a yanzu, zai yi nazari ga makomar siyasarsa kafin daukar matakin da ya dace nan gaba a yayin jawabin na sa.
Ana kallon yar da kwallon mangwaron cikin APC a bangaren na Atiku na zama kololuwar wani rikicin cikin gidan da ya kalli kokari na rushe kamfanonin da ya ke takama da su da nufin hana shi tashi a nufin cika burinsa na shugabantar Najeriya a nan gaba kamar yadda masu sharhi ke cewa.Yanzu dai kallo ya koma sama inda ake sauraron mataki na gaba da zai dauka a cikin guguwar da ke kara kadawa ta siyasa da ke nuna irin rikicin da ake fama da shi a cikin manyan jam'iyyu biyu na Najeriya.