Atiku Abubakar ya sake komawa PDP
December 4, 2017Talla
Atiku Abubakar dai ya yi wani bidiyo a shafinsa na Facebook inda ya ce ya sake komawa jam'iyyar ta PDP saboda gazawar jam'iyyar APC mai mulki wajen cika alkawuran da ta yi wa al'ummar Najeriya tun bayan da ta hau kan karagar mulki a shekarar 2015.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da Atikun ke sauya sheka, ya bar PDP ya yi takara a ACP a 2014 a lokacin ya ce jam'iyyar ta PDP ta gaza. Ya dai nemi shugabancin na Najeriya karkashin jam'iyyu uku idan aka koma tarihi tun daga shekarar 1993.