Atiku Abubakar ya koma Nijeriya bayan hutu na wata daya
January 21, 2007Talla
Mataimakin shugaban Tarayyar Nijeriya Alhaji Atiku Abukakar wanda a cikin watannin bayan nan ke fama da rashin jituwa da shugaba Olusegun Obasanjo, ya koma Nijeriya bayan wani hutu na wata daya a kasar Amirka. Da farko an yi ta yada jitajitar cewa Atiku ba zai ma koma Nijeriyar ba. A yau da rana mataimakin shugaban kasar ya sauka filin jirgin sama na babban birnin tarayya Abuja a cikin wani jirgin sama da ya chata, kuma kai tsaye daga nan ya wuce gidansa na gwamnati. ´Yan sanda sun hana da yawa daga cikin magoya bayansa shiga harabar filin jirgin saman don tarbarsa. Hakazalika an kuma hana manema labarai da wasu manyan jami´an gwamnati zantawa da Atiku Abubakar a lokacin da ya isa.