Atiku: Kokarin inganta rayuwar talakawa
February 14, 2019Tun daga jamhuriyya ta Uku ne dai aka fara jin duriyar madugun na adawa yayin da ya nemi zama shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar SDP
Kuma babban burin gwagwarmayar ta siyasa dai a fadar Abubakar din da zai ja ragamar 'yan lemar ya zuwa fafatawar dai bata wuci neman inganta rayuwar talakawa na kasar ba inda yake ikirarin kwato kansa ciki.
Atikun da har ila yau ke zaman tsohon jami'in hukumar hana fasa kwauri ta Kwastam dai ya taka rawa daban daban cikin fagen siyasar tarrayar Najeriyar cikin tsawon shekaru 26, kafin kaiwa ga zama dan takarar da ke da burin kwace goruba a hannun kuturu, a cikin zaben mai tasiri.
Tuni dai Atikun da ake yiwa kallon babban mai iImani a cikin tsari na kasuwa alkali, da kuma ya dora daukacin yakin neman zaben nasa ga farfado da tattali na arzikin tarrayar Najeriyar, ya tada kura a ruwa bayan bayyana aniyarsa ta cefanar da kamfanin man kasar na NNPC da ke zaman babbar giwa mai nama ga kasar.
Babban kalubalen da yake shirin fuskanta in har yai nasarar zaben dai na zaman gaggarumin rashin tsaron da ake ta'allakawa da rshin aikin yi da kuma kwararar makamai daga yankin Sahel
Kuma a tunanin Atikun da ya karade lunguna da sassa na kasar da nufin neman kuri'a dai masu tsintsiyar APC sun kasa ga muhimman batun rashin tsaro da ma yaki da talaucin da ke zaman alkawarinsu da 'yan kasa.