ASEAN: An gargadi Koriya ta Arewa kan kera makamin nukiliya
March 18, 2018Talla
Shugabanin yankin wato ASEAN sun yi wannan jan kunnen ne a yayin da suka soma zaman taron da suke yi duk shekara shekara. Sun nuna damuwa kan matakin da Koriya ta Arewa ta dauka na ba gudu ba ja da baya a batun kera da kuma gwaje-gwajen makaman nukiliyan duk da barazanar da hakan ke yi ga zaman lafiya a duniya.
Taron ya kuma nemi kasashe da suka kasance mambobi karkashin Majalisar Dinkin Duniya da su sanyawa Koriya ta Arewa takunkumi in har ta yi watsi da wannan kira. Taron kolin na bana na gudana a kasar Australiya inda Firaiministan kasar, Malcolm Turnbull ya kasance mai masaukin baki.