1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Arangamar Falasdinawa da Isra'ila kusa da Al Aqsa

Mahamud Yaya Azare
July 21, 2017

Falasdinawan da ke adawa da killace masallacin Al-Aqsa sun yi ta dauki-ba-dadi da jami'an tsaron Isra'ila a yankunan Falalsdinawa da wasu kasashe da ke adawa da killace masallacin na uku mai daraja a duniya.

https://p.dw.com/p/2gzMB
Jerusalem Konfrontationen
Hoto: Picture alliance/dpa/M. Illean/AP

An yi ta artabu tsakanin jami'an tsaron Isra'ila kimanin 2000 da aka jibge su a farfajiyar masallacin na Al-Aqsa mai Alfarma, da kuma dubban Falasdinawan da ke fusace da shiga kwana na 9 da killace masallacin da Isra'ila ta yi, yadda ta sanya kofofi da shingayen karfe gami da na'urorin caje masallata, wadanda ta ce, su din ma, sai tsofaffin da suka haura shekaru 50 kadai ne za ta amince su shiga masallacin. Bayan da jami'an na Isra'ila suka yi nasarar hana su shiga masallacin, dubban masu zanga-zangar sun danna cikin farfajiyarsa, yadda sukai Sallar Juma'a, kana tare da rera taken kalubalantar matakin na Isra'ila da shan alwashin sadaukar da rayukansu don 'yanta masallacin na Al-Aqsa. Khalid Hamdallah, kusa ne a kungiyar Jihadil Islami:

“Wannan zanga zangar sako ne  ga Isra'ila dama sauran duniya cewa, har abada,  Falasdinawa ba za su saryantar da hakkinsu na cikakkiyar mallaka da iko da masallacin Al-Aqsa mai alfarma ba. Daga yau za mu fara zaman dirshan din sai Baba-ta-gani a wannan farfajiya, har sai an dage shingaye a kofofin wannan masallaci mai Alfarma”

Ismail Haniya, Anführer der Hamas
Ismail Haniya, jagoran Hamas a yankin Zirin GazaHoto: Getty Images/AFP/S. Khatib

Atiyyah Sahuodi, jigo a kungiyar Al-Fatah ta Hukumar Falalsdinawa, ya nemi Majalisar Dinkin Duniya da kasashen da Isra'ila ke saurarawa, da su matsa mata lamba kan ta daina abin da ya kira “hauka marar iyaka” a yankunan Falasdinawa. Shugaban kungiyar Hamas da ke iko da yankin Zirin Gaza, Ismael Haniyyah, ya dora alhakin abin da ya kira “cin fuska da renin da Isra'ila ke yi wa Falasdinawa da wuraren ibadar musulmi masu alfarma” ga yaye bayan da shuwagabanni da jagororin Larabawa ke yi wa al'ummar ta Falalsdinawa a yanzu: “Mun yi amannar cewa, gangancin da makiyiyanmu Isra'ila ke yi kan masallacin Al-Aqsa, da ta'addancin da take wa al'ummar Falalsdinawa, ba ta isa ta yi su ba, ba don ta ga rashin hadin kan da ke tsakaninmu ba, da kuma yadda muka shagaltu da yakar juna”

Unruhen in Bethlehem und Jerusalem
Hoto: Picture-Alliance/dpa/N. Shiyoukhi/AP

Baya ga yankunan na Falalsdinawa, su ma al'ummomin sassa daban-daban na kasashen Larabawa sun taya Falasdinawan wannan zanga zangar, duk kuwa da haramta zanga-zangar da aka yi a galibin kasashen Larabawa, wadanda wasu daga cikin shuwagabanninsu da suka zake, ke daukar tayar wa da Isra'ila kayar baya ta'addanci ne.