1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Arangama da 'yan Shi'a a Najeriya

October 12, 2016

Bikin Ashura a Najeriya ya gamu da fito-na-fito a birane da dama inda aka dau matakan haramta jerin gwano da mabiya Shi'a suka saba yi a kowace shekara da kuma laccoci da suke kira Muzahara

https://p.dw.com/p/2R9wE
Nigeria Demo für die Freilassung von Ibraheem Zakzaky
Hoto: picture alliance/AP Photo/M. Giginyu

Al'ummar birnin Kaduna a yanzu haka na cikin zaman dar-dar bayan da wasu matasa masu zanga-zanga suka koma gidan shugaban 'yan Shi'a a birnin na Kaduna, inda ake rade-radin mutuwar mutane biyu. A cewar wakilin DW wannan na wakana ne a daidai lokacin da hukuma, ta baza jami'an tsaron 'yan sanda da sojoji domin hana 'yan Shi'ar gudanar da jirin gwanon da suka saba shiryawa a ranar Ashura a kowace shekara.

A birnin Kano ma jami'an tsaron sun yi arangama da mabiya tafarkin Shi'a da ke muzahara ta jimamin ranar da aka hallaka Imam Hussein bin Ali, daya daga cikin jikokin Annabi Muhammadu (SAW). 

Wakilinmu da ke Kano din Nasir Salisu Zango ya rawaito mana cewar mutane sun yi ta bin duk wanda aka gani sanye da bakaken kaya da ke zaman tufafin 'yan Shi'ar na al'ada, ana dukansu har ta kai da dama daga cikin 'yan Shi'an suka nemi mafaka a cikin asibitin Murtala da ke birnin na Kano.

Wannan lamari dai ya yi sanadiyyar jikkatar 'yan Shi'a din da dama. Gabannin aukuwar hakan dai, rundunar 'yan sandan jihar ta Kano ta fitar da sanarwar hana wannan muzahara, domin tabbatar da doka da oda. Amma mabiya Shi'a din suka yi biris da wannan sanarwa. Wani da ke cikin tawagar ta Shi'a, ya bayyana takaici bi sa yadda ake kokarin hana su gabatar da ibadarsu.