1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jiga-jigan APC sun zargi Tinubu da watsi da su

Ubale Musa ZUD/USU
September 29, 2022

Wasu gwamnoni da jiga-jigan jam'iyyar APC sun zargi kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Bola Ahmed Tinubu da watsi da su a jerin mutanen da aka tsara za su tallata takararsa.

https://p.dw.com/p/4HXDh
Dan takarar shugaban kasa na APC Bola Ahmed Tinubu
Dan takarar shugaban kasa na APC Bola Ahmed TinubuHoto: Stefan Heunis/AFP/Getty Images

Uwar jam'iyyar dai ba ta tsira ba, haka su ma wasu gwamnoni sun yi korafin an ware su, ko bayan masu takarar da ke neman komawa 'yan kallo, duk a cikin kokari na kaddamar da yakin neman zabe a cikin jam'iyyar APC wacce ke mulkin Najeriya tun shekara ta 2015.

Wata wasika daga shelkwatar jam'iyyar APC dai ta zargi Bola Ahmed Tinubu da karya alkawarin da ke tsakaninsa da jam'iyyar, alkawarin kuma da shugabancin jam'iyyar ya ce ya idan aka mutunta shi zai hada kai tare da aiki a tsintsiya madaurinki daya wajen nemannasarar APC.

Lokacin da jam'iyyar APC ta bai wa Tinubu takarar shugaban kasa
Lokacin da jam'iyyar APC ta bai wa Tinubu takarar shugaban kasaHoto: Nigeria Prasidential Villa

Ko bayan jam'iyyar dai babu ko guda cikin manya na masu takarar jam'iyyar a zaben fidda gwani na shugaban kasar cikin kwamitin yakin neman zaben Tinubun, a wani abun da wasu ke fassarawa da nuna alamu na wariya ta Tinubun a bangare na abokai na adawa.

Abdurrahaman Baffa Yola, daya a cikin masu ba da shawara ga mataimaki na shugaban kasar da kuma ya zuwa yanzun suka koma'yan kallo a cikin yakin neman zaben.

''Gaskiya an yi kuskure. Duk da cewa da mu da mataimakin shugaban kasa babu wanda ya yi magana kan abin da ya faru, amma akwai alamun tunani mara kyau domin an yi takara da mu a APC.'' Yola ya shaida wa DW.

Rikici ya dakatar da kaddamar da yakin neman zabe

Kokari na nuna wariya cikin jam'iyya ko kuma neman mafita ya zuwa daukar mulki dai, sannu a hankali sabon rikicin na neman tasiri a tsakani na masu tsintsiyar da ke neman fadawa rudu yanzu.

Kawo yanzu dai APC ta gaza sanar da ranar kaddamar da yakin neman zabenta, haka kuma an gaza kai wa ga tabbatar da tsarin da kowa ke fatan tafiya a kan sa.

To amma a fadar Bashir Ahmed da ke zaman daya a cikin mataimaka na daraktocin yakin neman zaben ta kafafe na zamani, dan takarar na shirin da ya buda domin daukar ra'ayin kowa ya zuwa nasara.

Rikicin cikin gida na APC dai na zuwa ne daidai lokacin da jam'iyyun adawar kasar irinsu PDP da NNPP da jam'iyyar Labour ke kara azama wajen ganin sun kayar da ita a zaben shugaban kasa na Fabrairun 2023.