Najeriya: Kokarin sasanta 'yan majalisar APC
April 17, 2019Duk da jam'iyyar APC ta yi nasarar rinjaye a cikin majalisun kasar guda biyu a shekara ta 2015 dai daga dukkan alamu masu adawar PDP sun ci karensu har gashinsa a cikin harkoki na majalisun kasar guda biyu da ke shirin karewa.
'Ya'yan PDP dai sun yi nasarar dakile kasafi, sannan kuma sun iya kaiwa ga kuntata wa manufofi na masu tsintsiyar kafin daga baya daukaci na shugabancin 'yan dokar ya sa kafa ya bar APC tare da komawa ga adawa.
Abun kuma da ya bata ran 'yan mulkin na Abuja da a halin yanzu ke neman hanyar toshe duk wata kafa ta tasirin PDP a wajen zabe da ma kila tafi da shugabancin majalisar ta tara da ake shirin girkawa.
Wani taron shugaban kasar da zababbun wakilan APC 233 dai, ya kare tare da yanke hukuncin inda suke shirin mika mukaman nasu da nufin tabbatar da al'ada ta tuwona maina a cikin majalisar a nan gaba.
Wakilai guda bakwai kacal dai APC ke da bukata da nufin gagarumin rinjaye a cikin harkokin majalisar, to sai dai kuma duk wani karamin kuskure na iya sauya akalar lamura a majalisar tare da kila maida ta zuwa hannu na adawar.