1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a tuhumi 'yar tsohon shugaban kasar Angola

Adrian Kriesch RGB/MNA
February 3, 2020

Shugaban Angola Joao Lourenco ya karyata batun shiga yarjejeniya da 'yar tsohon shugaba Isabel dos Santos don dawo da makudan kudaden gwamnati da ta karkatar don amfanin kanta.

https://p.dw.com/p/3XCzH
Shugaban kasar Angola João Lourenço, yayin hira da DW a birnin Luanda
Shugaban kasar Angola João Lourenço, yayin hira da DW a birnin LuandaHoto: DW/M. Luamba

A kasar Angola, gwamnatin kasar ce ta kaddamar da yaki da rashawa, inda ta soma da kama manyan jami'an gwamnati da ake zargi da laifuka na cin hanci. An kuma tanadi matakai na kwato kudaden kasar daga wasu da ake zargi da wawashe kudadden gwamnati, ciki har da  'yar tsohon shugaban kasar Isabel dos Santos, amma yanzu akwai batun cewa an shiga yarjejeniya da ita don ta maido da wasu daga cikin kudaden. Sai dai a tattaunawa da DW, shugaban kasar Joao Lourenco da ya gabatar da yakin na ba sani ba sabo ya karyata batun tare da yin karin haske kan lamuran da suka shafi yaki da rashawar.

Wani rahoton binciken da aka gudanar ya bayyana yadda Isabel dos Santos ta yi amfani da mukamin babanta Jose Eduardo dos Santos, wajen azurta kanta, a yayin mulkinsa na kusan shekaru 40. Matar dai ita ce ta fi ko wacce mace yawan dukiya a nahiyar Afirka. DW ta tambayi shugaban kasar kan batun shiga yarjejeniya da 'yar tsohon shugaban don mayar da wasu daga cikin kudaden, sai dai ya ce labarin na kanzon kurege ne.

Isabel dos Santos da wata kotu a Angola ta ba da umarnin dora hannu kan dukiyoyinta
Isabel dos Santos da wata kotu a Angola ta ba da umarnin dora hannu kan dukiyoyintaHoto: AFP/M. Riopa

''Wannan labarin bai da tushe kuma muna son mu tabbatar da cewa, babu wata yarjejeniya da aka kulla, ai mun bayar da dama ga wadanda aka samu da laifin cin hanci na watanni shida na su dawo da kudaden da suka sace ko suka fitar daga kasa ba bisa ka'ida ba. Saboda haka duk wanda bai yi amfani da wannan damar a can baya, dole yanzu ya fuskanci fushin hukuma.''

DW ta dora da batun ko shugaban yana tunanin tuhumar mahaifin Isabel kuma tsohon shugaban kasar Jose Eduardo dos Santos bisa laifuka na cin hanci da rashawa da ya yi a yayin mulkinsa? Shugaba Lourenco ya ce wannan sai a bar wa doka.

"Aikin bangaren shari'a ne, ba dan siyasa ke tuhumar mai laifi ba, in har ma'aikatar shari'ata ta gudanar da bincike ta gano laifi dole ta yi aikinta. Mu namu mu samar da kafa da kuma tsari na sauyi da walwala a fannin shari'a don ta samu damar gudanar da aikinta, amma ba hurumi na ba ne a matsayin shugaban kasa na soma tisa keyar jama'a kotu, ba ni ma da lokacin yin hakan don akwai wasu muhimman batutuwa a gabana da suka fi shafar kasa.''

Duk da arzikin man fetir Angloa na fama da karayar tattaln arziki saboda matsalar rashawa
Duk da arzikin man fetir Angloa na fama da karayar tattaln arziki saboda matsalar rashawaHoto: DW/Borralho Ndomba

Shugaban dai ya rike mukamin sakatare na babban jama'iyyar kasar ta MPLA a karkashin mulkin shugaba Jose Eduardo dos Santos da kuma ministan tsaron kasar, gwamnatin da ake zargi a karkashinta an tafka cin hanci da rashawa. Wannan ya sa DW ta tambayi shugaba Lourencos dalilin da ya sa bai fito ya kalubalanci gwamnatin a wancan lokacin ba.

"Shakka babu na yi aiki a karkashin tsohon shugaban kasar Jose dos Santos da ya kwashi tsawon shekaru 40n yana mulkin kasar, kuma duk muna ji muna ganin yadda lamura suke gudana, amma wadanda ya dace su yi abin da ya dace na nan dabam, sun fi mu da ma da sanin komai.''

Tun bayan ya dare mulki shugaban ya soma gabatar da sauye-sauye, daga ciki akwai batun na yakar rashawa inda ya kama da dama daga cikin manyan jami'an gwamnati.