Angela Merkel ta kai ziyara a sansanin 'yan Nazi
December 6, 2019Merkel ta shiga sansanin ne tare da rakiyar Firaministan Poland Mateusz Morawiecki da wakilan al'ummar Yahudawa da kuma guda daga cikin wadanda suka tsira da ransu bayan sun sha azaba a sansanin 'yan Nazin da ke da shekaru 87 a duniya.
Ziyarar ta Merkel na zuwa ne a daidai lokacin da batun kyamar Yahudawa ya sake kunno kai a nahiyar Turai, a yayin da a hannu guda rashin cikakkun shedu na zahiri ke yin kafar ungulu ga batun mika kundin cin zarafinsu da ake shirin gabatarwa.
Gabanin kai wannan ziyarar dai shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta bayyana matakin ware kudi kimanin miliyan 60 na Euro, domin tallafawa gidauniyar Auschwitz-Birkenau domin kula da sansanin da aka halaka mutane fiye da miliyan daya, galibinsu Yahudawa a tsakanin shekararun 1940 zuwa 1945.