1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana sukar shigar malamai siyasar Najeriya

Ibrahima YakubuFebruary 18, 2015

Kungiyoyin Mata a Najeriya sun nuna bacin ransu kan yadda 'yan Siyasa ke gayyatar Malaman Addinai wajen shirya masu tarurruka

https://p.dw.com/p/1Edqz
Wahlkampf in Nigeria 2015
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Kungiyoyin Mata a Najeriya sun nuna bacin ransu kan yadda 'yan Siyasa ke gayyatar Malaman Addinai wajan shirya masu tarurruka, domin samun goyan bayanda zumar Ganin Malaman sun taimaka masu wajan tallatasu a wuraren ibadu da kuma ganin sun cusawa mabiyansu 'yan Takaranda suke so

Yanzu haka dai saban salun da wasu 'yan siyasa suka bullo da shi wajen tallata kansu da jam'iyyarsu shi ne na janyo hankalin malaman addinai domin samun goyan baya da zummar ganin malaman sun taimaka masu wajen tallatasu a masallatai da coci-coci, tare da kuma ganin sun cusa wa mabiyansu akidojin jam'iyyar da dan takaran. Mrs Viki Bonaface, wata mai gwagwarmayar kwatowa al'umma 'yancinsu ta ce "Ba mu gamsu ba da yadda Malamai ke zuwa tararrakan siyasa da 'yan siyasar kasar ke shiryawa."

Rahotanni sun yi nuni da yadda wasu gwamnoni ke bai wa malaman addinai makudan kudade, da suke zuwa suna kaddamar da wani dan siyasa na amincewa masa da yin tazarce, lamarin da ke nuni da yadda a karshe a kan raba kudi ake ba iwa hammata iska.

Mallam Abdullahi bayero shi ne dai kakakin kungiyar majalisar koli ta tabbatar da shiri'ar Musulunci a Nigeria da ke nuna takaicinsa.

Nigeria Wahlen 2011 Bild 1
Hoto: DW/Gänsler

Shima dai Pastor Yohanna Buru shugaban cocin Christ evengelical intercessary fellowship a Nigeria kira ne yayi ga pastoci da malaman da 'yan siyasa ke anfani da su wajen cusawa jama'a dan takara.