1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana son ICC ta binciki Isra'ila kan kisan Falisdinawa

Ramatu Garba Baba
May 22, 2018

Ministan harkokin cikin gida na yankin Falisdinu Riyad al-Maliki ya nemi kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC da ta soma binciken Isra'ila kan kisan Falisdinawa sittin a rikicin zirin Gaza na makon da ya gabata.

https://p.dw.com/p/2y902
Niederlande - Internationaler Strafgerichtshof
Hoto: Imago/P. Seyfferth

Riyad al-Maliki da ya gana da Fatou Bensouda mai shigar da kara a kotun ta ICC da ke birnin Hague na kasar Netherland, ya nemi ta shigar da koken gaban kotun don ganin kotun ta yi aikinta na bincike da hukunta wanda aka samu da hannu a kisan. Ya ce yin hakan na da matukar mahinmanci ga al'ummarsa da suka kwashi shekara da shekaru suna fuskantar cin zarafi iri-iri daga jami'an tsaron Isra'ila.

Ganawa a tsakanin al-Maliki da Bensouda na zuwa ne bayan mutuwar wasu Falisdinawa guda sittin da ake zargin sojojin Isra'ilan da yi a yayin zanga-zanga da ta barke a zirin Gaza don adawa da matakin Amirka na mayar da ofishin jakadancinta birnin Kudus a makon da ya gabata.