1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Taron koli kan yanayi ya kammala a Glasgow

Abdoulaye Mamane Amadou
November 14, 2021

Hukumomi dabam-daban na tofa albarkacin bakinsu kan taron koli da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya kan sauyin yanayi da ya cimma matsaya ta bai daya, bayan mako biyu ana muhawara.

https://p.dw.com/p/42y8S
UN-Klimakonferenz COP26 in Glasgow
Hoto: Christoph Soeder/dpa/picture alliance

Taron na birnin Glasgow da aka yi wa lakabi da Cop26 dai bai cimma mata takamamiyar matsaya kan batun rage fitar da hayaki mai tiriri mai zafi da ke dumama yanayi ba da manyan kasashen duniya ke amfani da shi, hakan da batun kudaden tallafi ga kasashe matalauta da matsalar sauyin yanayi ke yiwa illa kai tsaye kamar yadda aka bukata tun daga farko, to amma sai dai taron ya bukaci kasashen duniya da su kara matsa kaimi wajen rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da ya nuna rashin cikakkiyar gamsuwa kan yarjejeniyar, ya ce lokaci yayi da takamata a dauki matakai na gagawa saboda matsalar sauyin yanayi na kara zama wata babbar barazana.

Shugabar hukumar EU Ursula von der Leyen ta ce duk da hakan taron ya kama hanyar cimmam muhimman muradan da aka sakawa gaba, sai dai ita kuwa matashiyar nan yar fafatukar kare muhalli Greta Thunberg, ta kira yarjejeniyar da "bla, bla, bla".