Ana jiran sakamakon zaben shugaban kasa a Chadi
April 11, 2016A ranar Lahadi 'yan kasar Chadi suka gudanar da zaben shugaban kasar wanda ake ganin zai bai wa Shugaban kasar mai ci Idriss Deby Itno damar sake darewa kan karagar mulki a wani sabon wa'adin mulki na biyar. Sai dai tuni kungiyoyin fararan hula suka nuna tababarsu ga sahihancin zaben kamar yadda Jean Bosco Manga daya daga cikin masu magana da yawun gamayyar kungiyoyin fararan hula na "Trop c'est trop" na kasar ta Chadi ya yi tsokaci:
"Babu tantama sakamakon da zai fito, sakamako ne na jeka na yi ka, domin tuni da ma gwamnati ta yi tsarinta na magudi don lashe wannan zabe. An yi takardun zabe na jabu, an katse layukan intanet da kuk wasu abubuwa da muka yi zaton za su faru don cimma mugunyar manufa."
Kasar ta Chadi dai na taka rawar gani wajen yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda irin su Boko Haram, da Al-Qaida a yankin Sahel.