Ana gudanad da bincike kan cutar ALZHEIMER a jami'ar Bonn.
October 26, 2006A nan Jamus da ma dai nahiyar Turai baki ɗaya, yawan tsoffin mutane sai ƙaruwa yake ta yi, yayin da ake ta kuma samun ƙarancin haihuwa. Jami’an kiwon lafiya dai sun bayyana cewa, yawan tsoffi masu kamuwa da cutar ta Alzheimer, shi ma sai ƙaruwa yake yi. Alƙaluma dai na nuna cewa kusan kashi 2 cikin ɗari na mutane masu shekaru 65 da haihuwa ne ke kame da cutar a nan Jamus. A nau’in masu shekaru 70 da haihuwa kuwa, yawan masu kame da cutar ya kai kashi 3 cikin ɗari. Sama da haka kuma, wato a cikin masu shekaru 75 da haihuwa, kashi 6 cikin ɗari ne ke fama da Alzheiman. Bisa alƙaluman dai har ila yau, an fi samun yawan masu kamuwa da cutar a jerin waɗanda suka kai shekaru 80 zuwa 85 da haihuwa. A nan Jamus kawai, yawansu ya kai kashi 25 cikin ɗari. Abin lura, wanda kuma likitoci ke nanatawa a nan shi ne, ana samun koma bayan wannan illar a nau’in masu fiye da shekaru 85 da haihuwa. Dalilin haka kuwa inji su, shi ne, mafi yawan masu kamuwa da cutar, suna mutuwa ne kafin su kai shekaru 80 ko sama da haka.
Gaba ɗaya dai alƙaluman sun ce a halin yanzu, fiye da mutane dubu ɗari 9 ne ke fama da wannan cutar ta Alzheimer ko kuma wasu cututtuka masu jiɓinta da ita. Game da hakan ne dai wasu masana kimiyya a jami’ar nan Bonn, suka fara gudanad da wani bincike don gano jiɓintar da ake da ita tsakanin irin abincin da mutum ke ci da kuma cutar.
Babban likita a asibitin horad da likitoci na jami’ar Bonn, Farfesa Frank Jessen, wanda ƙwararen masani ne a kan wannan cutar, ya bayyana cewa:-
„Da farko masu cutar na husakantar ɓacin tunani ne da yawan mantuwa. Wato a ko yaushe suna samun matsaloli wajen tunawa da ababa da dama da suka auku, ko da ba da daɗewa ba ne ma. Wasu kuma na mantuwa ne da abin da suka sani tun da da can. Idan cutar ta ci gaba kuma, sai su rasa ma ko su wane ne da inda suke takamaimai. Wasu ma har cikin gidajensu da suka saba da su, ba sa iya kai kawo su kaɗai. A ƙarshe dai, idan cutar ta yaɗu sosai a jikin masu fama da ita, sai su kasa yin komai da kansu. Ko magana ma bas a iya yi.“
Shi dai Farfesa Jessen, yana gudanad da bincike kan cututtukar da ke janyo ɓacin tunani da kuma mantuwa a bainar tsoffin mutane. Ya ce hanyar da ta fi dacewa wajen iya magance wannan cutar, ita ce a gano ta tun da wuri:-
„Kasadar kamuwa da wannan cutar tana ƙaruwa ne da yawan shekarun mutum. Kazalika kuma ana iya gadarta. Wato wanda ke da ’yan uwa masu wannan cutar, ya fi waɗanda ba su da su kasadar kamuwa da ita. Sa’annan kuma akwai wasu larurori da dama, waɗanda aka gano cewa suna janyo illoli ga ƙwaƙwalwa. A lal misali hauhawar jini, da ciwon sukari, da yawan kitse a jijiya da kuma yawan ƙiba.“
Idan ba gano cutar tun da wuri ba, har ta zaunu sosai a jikin mutum, aka fara ganin alamun mara lafiyan ya fara yawan mantuwa, to da wuya magani kawai ya iya warkad da shi. Abin da magani zai iya yi a cikin wannan halin, shi ne jinkirta yaɗuwar cutar amma ba warkad da ita ba, inji Dr. Dieter Lütjohann, shi ma wani masanin haɗa magunguna a jami’ar ta Bonn. Ɗaya daga cikin dalilan da ke janyo cutar Alzheimer ɗin dai, shi ne taruwar yawan furotin a ƙwaƙwalwa. A halin yanzu dai Dr. Lütjohann, na gudanad da bincike ne a cibiyar nazarin ƙwayoyin jiki ta jami’ar Bonn, don samo ƙarin bayani game da illolin da hakan ke janyowa. Amma ko wace masaniya ake da ita yanzu game da kasancewar furotin ɗin a ƙwaƙwalwa? Dr. Lütjohann ya bayyana cewa:-
„Waɗannan furotin ɗin, idan sun taru, suna iya mamaye wani yanki na ƙwaƙwalwa, abin da ke hana ƙwayoyin ƙwaƙwalwar iya numfashi kamar yadda ya kamata. To hakan ne wasu ƙwayoyin ke mutuwa su kuma janyo mantuwa, wadda ita ce alamar da aka fi sani ta cutar.“
A zahiri dai, Dr. Lütjohann ya fi ƙwarewa ne a fannin binciken Cholesterine, wato kitsen nan da ke taruwa cikin jijiya, ya toshe wa jini hanyarsa. A wannan sabon binciken furotin a ƙwaƙwalwa da yake yi kuma, ya ce ya gano cewa, magungunan da ake mafani da su wajen sauko da hauhawar Choleterine ɗin, waɗanda aka fi sani da suna Satine, suna kuma iya rage kasadar kamuwa da cutar Alzheimer. Kamar dai yadda ya bayyanar:-
„Mun gano, daga binciken da muka yi kan ƙwayoyin gina jiki da kuma dabbobi cewa, idan aka cim ma nasarar rage yawan Cholesterin da ƙwayoyin ke ɗauke da shi, ko kuma na wani ɓangaren jikin dabbar da muka yi gwaji da ita, ta yin amfani da maganin Satin, to muna kuma iya lura da ragowar yaɗuwar ƙwayoyin cutar ta Alzheimer.“
To amma akwai kuma wata matsala a nan, inji Dr. Lütjohann, wadda ita ce, ƙwayoyin gina jiki da ake samu a ƙwaƙwalwa, su ma suna bukatar Cholesterin don su iya aikinsu kamar yadda ya kamata. Sabili da haka, a halin yanzu, matsayin da aka kai na gano jiɓintar Choletserin ɗin da taruwar furotin masu janyo cutar a ƙwaƙwalwa na da muhimmanci ƙwarai a binciken da ake gudanarwa.
Sanarwar da wasu masana kimiyya na cibiyar horad da likitoci ta jami’ar Tübingen da ke kudancin Jamus suka bayar, na cewa sun samo wani maganin allurar riga kafi ga cutar ta Alzeiheimer, ta janyo hankullan masu bincike daga sassa daban-daban na duniya zuwa nan Jamus. A gwajin da suka yi da dabbobi dai, masanan sun ce sun sami gagarumar nasara. Sai dai, allurar ba ta karɓi masu cutar Alzeieimer ɗin da aka jarraba maganin a kansu ba. Amma duk da haka, Farfesa Frank Jessen na jami’ar Bonn na kyautata zaton cewa za a sammi ci gaba a binjciken da ake gudanarwa a hallin yanzu, har ma a kai ga samo maganin warkad da cutar ta Alzheimer:-
„Akwai dai nasarori da dama da muka samu a wannan fafutukar. Idan dai muka ci gaba da kyakyawar fatarmu ta cim ma nasara a wannan aikin, to mai yiwuwa a cikin shekaru 5 zuwa 10 nan gaba, za mu iya gano hanyar magance wannan cutar.“