1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana cin zarafin mata a yankin tafkin Chadi

Abdul-raheem Hassan
September 3, 2018

Kungiyar kare hakkin yara Plan International ta ce akalla 'yan mata 500 na fuskantar tsangwama a gidajensu, yayin da wasu ke cikin kunci na cin zarafi a makarantu da sauran wurare a kasashen yankin tafkin Chadi.

https://p.dw.com/p/34ERA
Berlin - Konferenz zur humanitären Krise in der Region Tschadsee
Hoto: DW/A. S. Muhammad

Kungiyar ta fitar da rahoton ne a lokacin da kungiyoyin agaji suka fara taron kwanaki biyu a birnin Berlin na kasar Jamus kan halin tsaro da sauran batutuwa da tafkin Chadi ke ciki. Kungiyar Plan International ta ce yawancin yaran mata a kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi matsalar auren wuri ya hanasu ci gaba da karatu.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane miliyan 10 ne ke bukatar agaji a kasashen da ke yankin tafkin Chadi musamman a Arewa maso gabashin Najeriya, sakamakon matsalar rashin tsaro na Boko Haram.