Jami'ai na lalata da mata a Koriya ta Arewa
November 1, 2018Wani rahoton bincike na kungiyar kare kare hakin dan Adam ta kasa da kasa ta Human Rights Watch ya zargi jami'an gwamnati da 'yan sandar kasar Koriya ta Arewa da cin zarafin mata ta hanyar tilasta masu yin lalata da su ba tare da wani hukunci ya biyo baya ba.
Kungiyar ta Human Rights Watch ta ce ta tattara bayanan shaida daga wasu mata 54 na kasar ta koriya ta Arewa wandanda suka yi nasarar tserewa daga kasar tasu zuwa wasu kasashe na duniya inda wasunsu suka bayyana cewa a kowane dare na Allah jami'an da ke tsaron gidajen kaso na kasar na tsamo mata daga cikin wadanda ake tsare da su domin tilasta musu yin lalata da su.
Ko baya ga jami'an gwamnati da na 'yan sanda rahoton ya zano alkalai da sojoji da masu aikin gadin kamfanoni da kasuwanni da cibiyoyin sufuri daga cikin jerin mutanen da ke amfani da matsayin nasu wajen tilasta wa matan yin lalata da su ba tare da wani hukunci ya biyo baya ba daga bangaren mahukunta.