Ana ci-gaba da yin tashin hankali a Yemen
June 6, 2011Yan adawa a ƙasar yemen sun buƙaci a naɗa mataimakin shugaban ƙasar Abd-Rabbu Mansour Hadi a matsayin muƙaddashin shugaban ƙasar bayan ficewar shugaba Ali Abdallah Saleh zuwa ƙasar Saudiyya domin kula da lafiyar sa, a dai dai lokacin da sassan da basa ga maciji da juna a rigingimun ƙasar ke fafatawa a hannnu guda, da kuma ƙoƙarin cimma yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta a ɗaya hannun.
Wasu daga cikin Yemenawa sun nuna farin cikin su game da ficewar shugaban ƙasar zuwa Saudiyya domin neman magani. Sai dai har ya zuwa yanzu ana ci gaba jin ƙarar harbe-harben bindigogi a Sana'a, babban birnin ƙasar, inda dama musayar harbe-harbe a tsakanin dakarun dake goyon bayan shugaban ƙasar da kuma na ƙabilu ke ta yin bata kashi tun kimanin makonni biyun da suka gabata.Ofishin magoya bayan Sheikh Sadeq Al-Ahmar dake arewacin unguwar Hassaba ya bayyana kissar mayaƙar ƙabilar guda uku, ko da shike kuma jami'an da suka sanar da batun sun buƙaci a sakaya sunayen su bisa hujjar cewar ba'a basu izinin zantawa tare da manema labarai ba. Wannan dai na zuwa ne a yayin da shugaba Abdallah Saleh ke murmurewa daga aikin fiɗar da aka yi masa a ƙirjin sa bayan raunin daya samu daga makamin rokar da aka harba a fadar sa a ranar Jumma'ar da ta gabata - kamar yanda kakakin gwamnatin ƙasar ya tabbatar:' Ya ce, shugaba Ali Abdallah Saleh yana cikin kyakkyawan yanayi na kula da lafiyar sa, kuma ai tuni ya yi magana ta tashoshin telebijin na ciki da wajen ƙasar, kuma ziyarar daya kai ta duba lafiyar sa ce, nan bada daɗewa ba kuma zai komo ƙasar a cikin lokacin daya dace. Harkokin mulki suna tafiya yadda ya kamata, rundunonin tsaro suna tsaye da kafafun su. Bugu da ƙari kuma jita-jitar da wasu ke ya'yatawa cewar ƙasar za ta wargaje, wannan duk mafarki da tunanin da babu gaskiya cikin sa ne."
Akwai kuma wani yunƙurin da sassan da abin ya shafa ke yi domin ganin an cimma wata yarjejeniyar tsagaita buɗe-wuta bayan tsawon lokacin da mayaƙan ƙabilun suka ɗauka suna fafatawa da dakarun dake biyayya ga shugaba Saleh, fafatawar da kuma ta yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane 200 cikin makonni biyun da suka gabata, tare da tilastawa dubbannin jama'a tserewa daga matsugunan su. Tuni dama masu zanga-zangar ke ganin sun sami kyakkyawar dama ce ta sake tinkarar matsalolin ƙasar - a yanzu, kamar yadda wani mai fafutukar kare haƙƙin jama'a ke cewa:
"Ya ce, a matsayin mu na waɗanda ke da hannu dumu-dumu cikin wannan juyin halin, ina ganin ficewar sa ta kasance ta har abada ce, kuma bisa la'akari da yanayin ficewar sa daga ƙasar, na tabbatar da cewar babu komawar da zai yi cikin ƙasa:"
Wasu manazarta a ƙasar ta Yemen na ganin cewar rauni da kuma ficewar shugaba Saleh sun samar da sabon yanayin da ita kanta Saudiyya da kuma ƙasashen yammacin duniya basu shirya masa bane, bisa la'akari da rawar da shugaban ke takawa a yaƙin da suke yi da ƙungiyar alQaidah a yankin, da kuma ƙin sanya hannun shugaban akan yarjejeniyar miƙa mulkin da ƙungiyar ƙasashen yankin Gulf suka tsara, kana 'yan adawar suka yi na'am da ita.
Abin jira a gani shi ne ko ita Saudiyya za ta kyale shugaba Saleh ya koma kan mulki, ko kuma za ta shawo kan sa ya sanya hannu akan yarjejeniyar domin warware matsalar cikin ruwan sanyi.
A ƙasa Za ku iya sauraron sautin wannan rahoto da kuma na wakilinmu dake a a birnin Alƙahira Mahammoud AzareYaya wanda ya yi mana nazari akan halin da ake ciki tsakanin Isra'ila da Falasɗinu.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Abdourahamane Hassane